Wata kotun tarayya a Amurka ta yanke wa wata ‘yar Najeriya mai suna Dr. Nkechy Ezeh hukuncin daurin shekaru 70 a gidan yari bayan samunta da laifin damfarar dala miliyan 1.4 da aka ware domin tallafa wa yara ƙanana da iyalai marasa ƙarfi.
Kotun ta bayyana cewa Ezeh ta karkatar da kuɗaɗen ƙungiyar Early Learning Neighborhood Collaborative (ELNC) wajen yawon shakatawa da bukukuwan iyali, tare da sanya wasu ‘yan uwanta a matsayin ma’aikatan bogi domin karɓar kuɗi ba tare da aiki ba.
Haka kuma an ƙara mata hukuncin shekaru 60 saboda kauce wa biyan haraji, tare da umarnin ta mayar da dala miliyan 1.4 da kuma dala 390,174 ga Hukumar Haraji ta Amurka (IRS).
Rahotanni sun ce bincike ya gano cewa an tura wasu daga cikin kuɗaɗen zuwa ga ‘yan uwanta da ke Najeriya.