An fara sanya labule tsakanin ɗalibai maza da mata a Jami’o’in Afghanistan

Ƙungiyar Taliban ta gabatar da sabbin sauye-sauye a Jami’o’in ƙasar, yayin da ɗalibai suka fara janyewa.

Kamar yadda BBCHausa ta bayyana, “ko da yake ɗalibai maza da mata za su ci gaba da zama a aji guda, sai dai an sanya labule a tsakaninsu, da zummar hana kowacce irin mu’amala a tsakani.

Daga yanzu dole ne kowacce daliba mace ta sanya doguwar riga (Abaya, sannan ta rufe fuskarta da Nikabi.

Dama an yi hasashen ganin irin waɗannan sauye-sauye, tun bayan da Taliban ta kwace iko”.

Comments (0)
Add Comment