Wasu hotuna da gidan rediyon Freedom Radio ta wallafa sun nuna cewa an fara sauya launin fentin wata makaranta da Bello Habib Galadanchi, wanda aka fi sani da Dan Bello, ya gyara tare da inganta ta, bayan wata ce-ce-ku-ce da ta taso kan zargin cewa launin fentin na da alaƙa da wata ƙungiya.
Lamarin dai ya jawo muhawara a tsakanin al’umma musamman a kafafen sada zumunta, inda wasu ke bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da batun launin fentin makarantar.
Zuwa yanzu dai, Dan Bello bai fitar da wata sanarwa ko yin magana kan lamarin ba. Sai dai da yammacin ranar Asabat ne aka samu wasu sababbin hotuna da ke nuna cewa an fara sauya launin fentin makarantar.