An kama matasa 10 da suka ɗaura wa kansu aure kan sadaki N3,000

Wani lamari mai cike da cece-kuce ya girgiza al’umma a jihar Bauchi bayan da wasu matasa suka shirya tare da ɗaura wa abokinsu aure da budurwarsa mai shekara 18 kan sadaki Naira 3,000 ba tare da bin ƙa’idojin shari’a da yardar iyaye ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama angon mai suna Muhammad Chindo da amaryarsa Kamila, tare da wasu abokansu guda takwas bayan umarnin da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya bayar na kamo duk waɗanda ke da hannu a lamarin.

An ce matasan, waɗanda ke zaune a unguwar Mahaukata a cikin garin Bauchi, sun shirya komai da kansu inda ɗaya daga cikinsu ya zama limamin daurin aure, wani ya tsaya a matsayin waliyyin amarya, yayin da wata budurwa ta kasance “uwar ɗaki”.

Shugaban ƙungiyar ’yan sintiri ta jihar, Alhaji Umaru Shayi, ya ce sai da aka shafe kwanaki biyar ana bincike kafin jami’ai su samu nasarar kamo mutum 10 da ke da alaƙa da auren.

Ya bayyana hakan ne lokacin da aka gabatar da matasan a gaban uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aishatu Bala Mohammed, wacce kuma ke jagorantar kwamitin yaƙi da cin zarafin jinsi a jihar.

Lamarin ya jawo taron gaggawa tsakanin jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da malamai domin tattauna matakin da ya kamata a ɗauka.

A nasa ɓangaren, Kwamandan Hisbah na jihar Bauchi, Mohammed Bununu, ya bayyana auren a matsayin mara inganci a shari’ar Musulunci, yana mai cewa mahaifin amaryar bai san da daurin auren ba.

Ya ce a Musulunci dole sai da yardar waliyyi da kuma cikakken sadaki kafin aure ya inganta, yana mai gargadin cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da irin wannan dabi’a ba.

Uwargidan gwamnan jihar ta yi Allah wadai da abin da ta kira “mummunar ɗabi’a”, tare da kira ga iyaye su ƙara kula da tarbiyyar ’ya’yansu da sanya ido kan rayuwarsu.

Ta kuma buƙaci sarakuna, malamai da ’yan jarida su ƙara wayar da kan matasa kan muhimmancin bin hanyoyin da suka dace wajen aure da zamantakewa.

Bayan shafe sama da sa’o’i biyar ana tattaunawa tsakanin iyayen yaran da kwamitin, an cimma matsayar miƙa lamarin ga rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, CSP Nafiu Habib, ya tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan lamarin, yana mai cewa bayan kammala bincike za a miƙa matasan ga Hukumar Shari’ar Musulunci domin ɗaukar matakin da ya dace.

Sai dai mahaifin angon, Malam Abdullahi Muhammad Dumi, ya roƙi gwamnati da ta taimaka wajen gyara auren maimakon kai yaran gidan gyaran hali.

Ya ce talauci da rashin halin yin aure ne ya jefa matasan cikin wannan hali, yana mai kira ga gwamnati ta samar da tsarin tallafa wa matasa masu son yin aure.

Comments (0)
Add Comment