An kama shugaban PDP na Ogun da wasu jami’an INEC bisa zargin sayen kuri’u a lokacin zaɓen cike gurbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wasu jiga-jigan yan jam’iyyar PDP guda biyu da kuma ma’aikatan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) guda biyu, bisa zargin sa hannu wajen yunkurin sayen kuri’u da kuma shirin ƙulla maguɗi a zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a mazaɓar tarayya ta Remo.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne da sassafe a ranar Asabar, kuma suna bayar da muhimman bayanai ga ‘yan sanda kan rawar da kowa ya taka domin cin hanci da karkatar da sakamakon zaɓen.

A wani ɓangaren kuma, jam’iyyar PDP ta jihar Ogun ta fito da sanarwa cikin gaggawa inda ta bayyana cewa an kama shugaban jam’iyyar na jihar, Tella, a otal ɗinsa, lamarin da ta bayyana a matsayin ƙudirin rage ƙarfinta a matsayin jam’iyyar adawa.

Jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa kama jiga-jiganta wani yunkuri ne da aka kitsa domin bai wa jam’iyyar APC mai mulki damar samun rinjaye ta hanyar karkatar da zaɓen cike gurbi a nata amfani.

Comments (0)
Add Comment