Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi ta kama wata mata mai shekaru 40, Fatimah Ibrahim, bisa zarginta dayin lalata da yaro mai shekaru 12 a Tashar Jama’are, da ke karamar hukumar Katagum.
Kwamishinan hulda da jama’a na ‘yan sandan, CSP Ahmed Wakil, ya bayyana cewa yaron, wanda dalibi ne a makarantar Islamiyya, yana zama tare da waccan matar ne inda ake zargin tana yi masa lalata har tsawon watanni biyu.
Yaron ya bayyana cewa matar na ba shi wani hadadden ruwan lemu kafin ta aikata masa danyen aikin, kuma hakan na faruwa ne idan a gidan babu wasu mutane.
Bayan kamata, Fatimah ta amsa laifinta, kuma tuni aka fara bincike domin gurfanar da ita a gaban kuliya.