An kama wata mata yar shekara 28 bisa jefa yar ta a cikin Masai a karamar hukumar Hadejia

Rundunar Hukumar Tsaro na Farin Kaya wato Civil Defence ta Kasa reshen Jihar Jigawa kama wata mata yar shekara 28 a Duniya mai suna Aishatu Yahaya, bisa jefa yar ta a cikin Masai a nan karamar hukumar Hadejia.

Kakakin hukumar SC Adamu Shehu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Dutse.

Comments (0)
Add Comment