Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran Boko Haram mai suna Bakura, a yankin Tafkin Chadi, inda ƙasar ke iyaka da Najeriya da Chadi da Kamaru.
A wata sanarwa da sojojin suka fitar a ranar Alhamis, an kashe Bakura ne yayin wani aikin soji a wani tsibiri a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijar a makon da ya gabata.
Bakura dai ya jagoranci wani ɓangare na ƙungiyar Boko Haram wadda ke biyayya ga tsohon shugaban ƙungiyar, Abubakar Shekau, inda ya ƙi shiga reshen abokan hamayyar su na ISWAP inda ya koma tsibirin da ke gefen Nijar na tafkin tare da mayaƙansa.
Sunan asali na Bakura shi ne Ibrahim Mahamadu, mai kimanin shekara 40 a duniya kuma ɗan asalin Najeriya ne.
Ya shiga Boko Haram sama da shekaru 13 da suka gabata, sannan ya karɓi shugabancin kungiyar bayan mutuwar Shekau a watan Mayu 2021.