An kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da jiragen yaki suka kai a Borno da Nijar

Rundunar sojin saman ta ce sassan jiragen Operation Hadin Kai da Whirl Punch a yankin arewa maso gabas da arewa ta tsakiya, sun kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da jiragen yakin suka kai a Borno da Nijar.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai, AVM Gabkwet, ya ce na’urorin da ake amfani da su na iska sun ci gaba da kakkabe ‘yan ta’adda tare da lalata gine-ginensu da kayan aiki, ta yadda za su takaita kai farmaki kan sojojin kasa da ‘yan Najeriyar da ba su ji ba ba su gani ba .

A cewarsa, an kuma lura da motocin bindigu guda bakwai da aka ajiye a karkashin bishiyoyi da ke cikin wannan wuri.

Yace ta wannan mataki, an rage karfin barayin mai na ci gaba dayin zagon kasa da lalata bututun mai.

Comments (0)
Add Comment