An rantsar da sabbin kwamishinoni 8 da majalisar dokokin jihar Ribas ta tantance

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas da majalisar dokokin jihar ta tantance ranar Talata.

An gudanar da bikin rantsar da sabbin kwamishinonin a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Fatakwal cikin daren jiya, sa’o’i bayan tantacewar majalisar.

Yayin da yake jawabai bayan rantsar da kwamishinonin, Gwamna Fubara ya yi kira a gare su su riƙa adana ayyukan da suka gudanar a ma’aikatunsu.

Gwamnan ya ce adana ayyukansu zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati a kowane mataki, musamman saboda hakan zai taimaka wa waɗanda za su gaje su a nan gaba, su san inda za su ɗora.

Fubara ya bayyana damuwarsa kan yadda ya ce tsoffin kwamoshinonin da suka ajiye aiki musamansu, suka kasa adana tarihin ayyukan da suka gudanar a ma’aikatunsu.

Comments (0)
Add Comment