An sallami mutumin da ya yi kwana 100 da zuciyar ƙarfe daga asibiti

Likitoci a Australia sun ce wani maras lafiya ya kafa tarihin zama mutum na farko a duniya da aka sallama daga asibiti da dasasshiyar zuciya, yayin da yake dakon samun zuciyar da za a yi masa dashe da ita.

Mutumin ɗan kimanin shekara 40, ya sake kafa wani tarihin inda ya rayu tsawon kwanaki 100 da wata na’urar ƙarfe kafin ya yi nasarar samun zuciyar mutum.

Likitocin sun ce suna fatan dashen na’urar ƙarfen wadda ke tunkuɗa jini zuwa sassan jiki da kuma huhu za ta maye gurbin buƙatar yi masa dashen zuciyar ma baki ɗaya.

– BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment