An sauke daraktotin matatun man fetur na Fatakwal da Warri da Kaduna

Sabuwar hukumar gudanarwa da shugabancin kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, karkashin jagorancin sabon Babban Darakta na kamfanin, Bayo Ojulari, da Musa Ahmadu-Kida a matsayin Shugaban Hukumar Zartaswa, sun sauke daraktocin matatun man fetur na kasa dake Fatakwal, Warri da Kaduna.

Haka zalika, wasu manyan jami’ai a cikin kamfanin sun rasa mukamansu, ciki har da Bala Wunti, tsohon shugaban NAPIMS, wani reshe na NNPCL.

Rahotanni daga cikin kamfanin sun tabbatar da wannan sauyi da aka yi, inda aka duk ma’aikatan da ya rage musu kasa da shekara guda kafin su yi ritaya, su ajiye aiki kafin lokacin.

Kawo yanzu, mai magana da yawun kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, bai fitar da wata sanarwa ba dangane da sauye-sauyen da aka yi.

Idan dai za’a iya tinawa, a watan Afrilu 2025, Shugaba Bola Tinubu ya sallami tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPCL, Mele Kyari, da tsohon babban daraktan kamfanin Chief Pius Akinyelure, inda ya maye gurbinsu da Ojulari da Ahmadu-Kida.

Comments (0)
Add Comment