An soki wani kudiri dake kokarin halasta amfani da tabar wiwi domin magani a malissa

Wani kudiri dake kokarin halasta amfani da tabar wiwi domin magani a jiya ya gamu da cikas a majalisar wakilai bayan kwamitin da aka dorawa alhakin tabbatar da kudirin ya bayyana adawarsa da kudirin.

Shugaban kwamitin kwayoyi na majalisar wakilai, Francis Agbor, yace kwamitin ba zai goyi bayan kudirin ba.

Francis Agbor ya sanar da haka a lokacin kare kasafin kudin hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA).

Shugaban hukumar, Buba Marwa, ya bayyana a gaban kwamitin domin kare kasafin kudin hukumar.

‘Yar majalisa Mariam Onuoha ta jam’iyyar APC daga jihar Imo, ita ce ta gabatar da kudirin neman halasta amfani da tabar wiwi domin magani a Najeriya.

Kazalika, shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa, na jam’iyyar APC daga jihar Kano, ya gabatar da wani kudirin dake bukatar tsaurara hukunci akan ‘yan kasuwa da masu safarar tabar wiwin tare da masu amfani da ita.

Dukkan kudirorin suna matakai daban-daban na tabbatar da su.

Comments (0)
Add Comment