An Yi Jana’izar Sojoji Uku Da Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Taka Bam A Isa, Jihar Sokoto

An gudanar da jana’izar sojoji uku daga cikin jami’an rundunar sojin Najeriya da suka rasa rayukansu bayan motarsu ta taka bam ɗin da ake zargin ƴan ta’adda sun dasa a kan hanyar Isa zuwa Bargaja a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin ke gaggawar kai ɗauki zuwa ƙauyen Bargaja bayan maharan sun kai hari da sanyin safiyar ranar Asabar. Sai dai motar sintirin da ke ɗauke da sojojin ta taka bam ɗin da aka binne a kan hanya, wanda ya haddasa fashewa tare da janyo asarar rayuka da raunata wasu jami’ai.

An yi jana’izar sojojin uku ne bisa tsarin soja, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan harin da kuma ƙoƙarin daƙile amfani da na’urorin fashewa (IED) da ƴan ta’adda ke amfani da su a yankin.

Lamarin ya sake nuna irin barazanar da hare-haren ƴan ta’adda ke ci gaba da haifarwa ga jami’an tsaro da ma al’ummomin yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Comments (0)
Add Comment