Ana ci gaba da kaɗa ƙuri’a a zaben shugaban kasar Chadi

An bayyana zaben a matsayin wani babban mataki da zai kawo karshen gwamnatin rikon kwarya ta kasar wadda ta kwashe shekaru uku.

An dai samu jinkiri wajen fara kada kuri’a, inda a wasu wuraren aka bude rumfunan zabe sa’a daya bayan lokacin da aka tsara.

Shugaban rikon kwarya Mahamat Deby ya kaɗa tasa kuri’ar a N’Djamena, babban birnin ƙasar.

Ya ce yana alfahari da cika alkawarinsa na mutunta wa’adin “zabuƙan da za su tabbatar an dawo da bin kundin tsarin mulkin kasar sau-da-kafa.”

Ya kara da cewa “Ya rage ga al’ummar Chadi su kada kuri’a kuma su zabi shugabansu da suka ga ya dace.”

Masu jefa kuri’a miliyan takwas ne ke zaben shugaban kasar daga cikin ‘yan takara 10 da suka hada da shugaban soji Deby da firaminista Succes Masra.

Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben ne a ranar 21 ga watan Mayu, amma za a iya zuwa zagaye na biyu a watan Yuni idan har ba a samu wanda ya samu nasara ba a zagayen farko na zaben.

Comments (0)
Add Comment