Ana fargabar ƙarin tashin farashin gas na girki a Najeriya

Ana ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar ƙarin tashin farashin gas na girki a Najeriya, yayin da ’yan kasuwa da masu amfani da gas ɗin ke fuskantar matsin lamba sakamakon tsadar kaya da ƙarancin wadata a sassa daban-daban na ƙasar.

Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Iskar Gas ta Najeriya, Nigeria Association of Liquefied Petroleum Gas Marketers (NALPGAM), ta bayyana cewa farashin gas ya ƙara tashi daga kusan naira 1,300 zuwa naira 1,500 kan kilo guda a wasu yankuna na ƙasar.

Ƙungiyar ta danganta matsalar da ƙarancin wadatar gas a tashoshin ajiya, tashin farashi daga kamfanonin samar da iskar gas, matsalolin sufuri da kuma ƙarin kuɗaɗen gudanar da kasuwanci.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce ’yan kasuwa na sayen tan 20 na gas kan sama da naira miliyan 25 zuwa miliyan 26, lamarin da ta ce ke ƙara wa masu amfani da gas ɗin nauyi.

NALPGAM ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati da masu ruwa da tsaki ba su ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya ƙara jefa gidaje da ƙananan sana’o’i cikin mawuyacin hali.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa tashin farashin gas na iya ƙara haddasa hauhawar farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi, musamman yadda gidaje da dama ke amfani da gas wajen girki da harkokin yau da kullum.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa ci gaba da tashin farashin makamashi na iya kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati na rage wahalhalun rayuwa da bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta a Najeriya.

Comments (0)
Add Comment