Ana Hasashen Farfesa Pantami da Magobayansa Za Su Koma Jam’iyyar APC Mai Alamar Rogo

Ana ta hasashen cewa magoya bayan Isa Ali Ibrahim Pantami za su iya yin sabon tsari na siyasa bayan janyewarsa daga zaɓen fidda gwani na APC a Gombe. Sai dai, har yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da cewa zai koma jam’iyyar APM mai alamar rogo.

Rahotanni sun nuna cewa Pantami ya fice daga zaɓen fidda gwani na APC ne saboda zargin rashin adalci da rashin bin ƙa’idojin zaɓe a cikin jam’iyyar.

A cikin sanarwar da aka fitar daga “Pantamiyya Movement”, an ce za su sanar da “mataki na gaba” a siyasa nan gaba, abin da ya sa mutane da dama suka fara hasashen yiwuwar sauya sheka.

Duk da haka, akwai wasu bayanai da ke nuna cewa Pantami har yanzu yana da alaƙa da APC, domin a farkon shekarar nan shi da magoya bayansa sun bayar da gudummawar miliyoyin kuɗi domin tallafawa rajistar APC a Gombe.

Comments (0)
Add Comment