Ana sa ran isowar jiragen ruwa 33 masu dauke da man fetur da sauran kayayyaki a Legas

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) ta sanar da cewa ana sa ran isowar jiragen ruwa 33 dauke da kayayyakin man fetur da sauran hajoji a tashoshin Apapa, Tin Can Island da Lekki Deep Sea Port da ke Jihar Legas daga ranar 30 zuwa 31 ga Janairu, 2026.

A cewar NPA, jiragen 22 daga cikin su na dauke da kwantena na kayayyaki daban-daban, yayin da sauran ke dauke da danyen mai, fetur, dizal, gasolin, bitumen da sauran kayan kasuwanci. Hukumar ta kuma ce a halin yanzu akwai wasu jiragen ruwa da dama da ke jiran sauka, yayin da wasu ke ci gaba da sauke kaya a tashoshin.

NPA ta bayyana cewa wannan na daga cikin kokarin tabbatar da wadatar kayayyaki da ci gaban harkokin kasuwanci a manyan tashoshin jiragen ruwa na kasar.

Comments (0)
Add Comment