Annobar amai da gudawa ta halaka mutum 8 fiye da mutane 200 kuma sun kamu

Annobar cutar amai da gudawa, wato cholera, ta sake bulla a jihar Zamfara, musamman a ƙaramar hukumar Bukkuyum, inda mutane fiye da 200 daga ƙauyuka 11 aka tabbatar sun kamu da cutar. Rahotanni daga mazauna yankin da ma’aikatan lafiya sun tabbatar da mutuwar mutum 8, tare da ƙarar rashin magunguna da rashin isassun kayan kiwon lafiya.

Cutar, wacce ke yaduwa ta hanyar shan ruwan da ya gurbace, ba sabuwar aba ba ce a Najeriya. A farkon shekarar nan, ta yi sanadin mutuwar gomman mutane a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto da Neja. Shekaru biyu da suka gabata ma, cholera ta barke a fadin kasar, inda ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a jihohi irin su Lagos da Kano.

Masana sun danganta yaduwar cutar da karancin tsaftataccen ruwan sha, musamman a ƙauyuka da biranen da ke fama da matsalar ruwa da rashin tsaftar muhalli. Wasu yankunan da cutar ta fi shafa sun haɗa da Nasarawa-Burkullu, Gurusu, da Dabka, inda yawancin masu cutar ke kwance a gida ba tare da samun kulawar likita ba.

Haka nan, har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga hukumomin jihar Zamfara dangane da sake ɓullar cutar.

Comments (0)
Add Comment