APC Ta Tsayar da 24 ga Yuni Domin Gudanar da Zaɓen Fidda Gwani a Mazabun da Aka Mayar, Ciki Har da Mazabar Aujara ta Jigawa

Jam’iyyar APC ta sanar da ranar 24 ga Yuni, 2026 a matsayin ranar gudanar da zaɓen fidda gwani domin fitar da ‘yan takara a sabbin mazabun majalisun da aka dawo da su a jihohin Benue, Delta, Jigawa da Kogi, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Matakin ya biyo bayan dawo da wasu mazabu da aka dade ba a gudanar da zaɓe a cikinsu, bisa umarnin kotuna da kuma tsarin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). A jihar Jigawa, Mazabar Aujara na daga cikin mazabun da aka dawo da su, wanda hakan zai bai wa al’ummar yankin damar sake samun wakilci a majalisar dokokin jihar.

A cewar jadawalin da APC ta fitar, za a fara sayar da fom da sauran shirye-shiryen cikin kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaɓen fidda gwanin a ranar 24 ga Yuni. Jam’iyyar ta ce matakin na da nufin tabbatar da kammala zaɓen cikin lokaci, daidai da jadawalin zaɓukan shekarar 2027.

Hukumar INEC ta riga ta umarci jam’iyyun siyasa su sanar da ita game da shirye-shiryen zaɓen fidda gwani a waɗannan mazabu, tare da bin ƙa’idojin dokar zaɓe.

Comments (0)
Add Comment