(ASUU), reshen Akure, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta tilasta musu shiga yajin aiki

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU), reshen Akure, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta tilasta musu shiga yajin aiki sakamakon matsalolin da jami’o’i ke fuskanta.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Jami’ar Tarayya, Oye-Ekiti (FUOYE), Shugaban ASUU na jami’ar, Farfesa Adeola Egbedokun, ya ce malaman sun yi haƙuri sama da shekaru biyu ba tare da shiga yajin aiki ba, suna jiran gwamnati ta cika musu alƙawura.

Ya bayyana bukatun ASUU da suka haɗa da:

Sake duba yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta 2009.

Soke tsarin rancen ɗalibai na TISSF da ASUU ke ganin zai jefa ɗalibai cin bashi.

Dakatar da kafa sababbin jami’o’i ba tare da tsari ba.

Inganta fanshon malamai da sauran ma’aikata.

Egbedokun ya zargi gwamnati da ɓata lokaci da kuma yin alkawuran karya.

Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali.

Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya.

Comments (0)
Add Comment