Atiku Abubakar Ya Ce Gwamnatin APC Ta Fi Mulkin Soja Muni

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su ne mafi muni da ya taɓa gani a kusan shekaru 40 da ya shafe yana siyasa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Abuja yayin bikin gabatar da littafin The Loyalist, wanda Bolaji Abdullahi, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya rubuta.

Atiku ya yaba da jam’iyyar ADC, yana mai cewa tana zama wata hanya ta haɗa ra’ayoyi da akidu daban-daban na siyasa daga faɗin ƙasar.

Ya ce: “Muna da wata dama ta musamman a cikin jam’iyyar ADC. Wuri ne da ra’ayoyin siyasa daban-daban daga ko’ina cikin ƙasar suka haɗu, domin sake haɗa Najeriya da kuma farfaɗo da tafiyar dimokiraɗiyyar mu.”

Da yake waiwaye kan halin da ƙasar ke ciki a ƙarƙashin gwamnati mai ci, Atiku ya ƙara da cewa:
“Idan akwai wani abu mai kyau a cikin ci gaban siyasar da muke gani a baya-bayan nan, to shi ne wannan haɗuwar da muke yi domin ceto ƙasar daga abin da nake ganin shi ne mafi munin gwamnati da na taɓa gani a kusan shekaru arba’in.

“Ko gwamnatocin soja kafin 1999 ba su lalata rayuwar ƙasa da tunanin al’umma kamar yadda wannan gwamnati ta yi ba.”

Ya kuma bayyana cewa da dama daga cikin waɗanda suka halarci taron sun taka rawa wajen kafa jam’iyyar APC, amma daga baya suka rasa ƙwarin gwiwa sakamakon yadda ta gudanar da mulki.

Atiku ya ce: “Da yawa daga cikinmu da ke nan mun kasance cikin waɗanda suka kafa APC; amma abin takaici, abin da muka yi tsammani zai ceci ƙasar bai faru ba.”

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su sake ɗaukar alhakin gina wata sahihiyar madadin jam’iyya ta siyasa.

Ya ce: “Kamar yadda muka taɓa ɗaukar alhaki muka haɗu muka kafa wata jam’iyya a baya, haka nan dole mu sake haɗuwa domin tabbatar da fitowar sabuwar ƙungiyar siyasa da za ta iya ceto wannan ƙasa domin amfanin al’ummarta.”

Comments (0)
Add Comment