Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan sauya sheƙar da abokin takararsa a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa, ya yi zuwa jam’iyyar APC.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba ya jin damuwa ko ɓacin rai game da sauya sheƙar Sanata Ifeanyi Okowa, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Atiku ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa ya ji ba daɗi kan mutumin da ya yi amfani da ƴancinsa na dimokuraɗiyya. “Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ba ya ɗaukar kowa da gaba, ya faɗa hakan kuma yana nufin hakan.
A matsayinsa na ɗan dimokuraɗiyya, yana mutunta ƴancin yin tarayya da yin zaɓi wanda shi ne ginshikin dimokuraɗiyya, ba tare da hakan ba, dimokuraɗiyya za ta zama ba ta da wata ma’ana.Ya kuma kara da cewa babu ƙamshin gaskiya a jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP