Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen fidda gwani a jam’iyyar ADC ya nuna cewa dimokraɗiyya na nan da ranta a Najeriya duk da ƙalubalen da take fuskanta.
Atiku ya bayyana hakan ne bayan lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a wani zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Abuja.
Ya ce yayin da wasu jam’iyyun siyasa ke nuna halayen da suka saɓa wa dimokraɗiyya, ADC ta nuna cewa har yanzu akwai damar gudanar da siyasa cikin gaskiya, adalci da bai wa kowa dama.
“Ina miƙa godiyata ga dukkan wakilan jam’iyyar da suka ba ni wannan dama ta wakiltar ADC a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Wannan babban abin alfahari ne a gare ni,” in ji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ADC ta shirya tsaf domin kare dimokraɗiyya da kuma ceto ƙasar daga abin da ya kira babbar barazana ga tsarin mulkin dimokraɗiyya tun bayan komawar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999.
A cewarsa, tsarin zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar ya bai wa kowane ɗan takara damar fafatawa cikin gaskiya ba tare da nuna wariya ko tilastawa ba.
Ya ce mambobin ADC sun nuna cewa suna mutunta ra’ayoyin juna tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe bisa ƙa’ida da adalci.
Atiku ya samu nasara a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na ADC bayan samun ƙuri’u 1,846,370, inda ya kayar da abokan takararsa, Rotimi Amaechi da Muhammed Hayatu-Deen.
Ya yi alƙawarin yin aiki tare da dukkan mambobin jam’iyyar domin ƙarfafa haɗin kai da kuma fuskantar babban zaɓen shekarar 2027.