Atiku ya bukaci Tinubu hana Seyi Tinubu shiga hurumin kungiyar dalibai ta kasa NANS

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakile yunkurin da dansa, Seyi Tinubu, ke yi na shisshigi cikin harkokin kungiyar dalibai ta kasa, NANS.

Atiku ya bayyana hakan ne bayan wani rahoto daga shugaban NANS, Atiku Isah, da ya zargi Seyi da kokarin ba shi cin hanci har naira miliyan dari domin ya rera wakar yabon gwamnatin Tinubu, wanda ya ce ya ki amincewa.

Seyi ya musanta zargin, yana mai cewa dukkanin kalaman na bogi ne kuma suna bata masa suna.

Atiku ya ce irin wannan zargi daga dan shugaban kasa na iya haifar da barazana ga dimokuradiyya, yana mai kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa don gano gaskiya.

Comments (0)
Add Comment