Atiku Ya Nemi Gwamnati Ta Yi Cikakken Bayani Kan Tsare El-Rufai, Yana Mai Nuna Damuwa Kan Lafiyarsa

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta fito fili ta yi bayani kan tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sakamakon rahotannin da ke cewa yana fuskantar matsalolin lafiya tare da takaita masa damar ganawa da iyalansa da lauyoyinsa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Atiku ya bayyana lamarin a matsayin “ damuwa ga iyalansa, abokansa da masu hulɗa da shi.”

Ya jaddada cewa gwamnati na da alhakin bayyana wa ’yan Najeriya gaskiya kan halin da ake ciki. “Dole ne ta fayyace wace hukuma ce ke tsare da shi shin Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), Independent Corrupt Practices Commission (ICPC), ko State Security Service (SSS), ko kuwa wata hukuma daga cikin hukumomin tsaro,” in ji shi.

Atiku ya yi gargadin cewa tsarewa a ɓoye kan haifar da shakku a tsakanin jama’a. Ya ce ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin gaskiya, inda ya ƙara da cewa duk wata hukuma da ke da alhakin tsare shi na da wajibcin kare lafiyarsa da mutuncinsa tare da ba shi damar samun kulawar likita da kuma ganawa da iyalansa da lauyoyinsa kamar yadda doka ta tanada.

Sanarwar ta biyo bayan zargin mai taimaka wa El-Rufai kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, wanda ya ce tsohon gwamnan ya zubar da jini ta hanci yayin da yake tsare a hannun EFCC.

Adekeye ya ce an yi masa tambayoyi kafin daga bisani a ba shi belin wucin gadi, amma har yanzu yana tsare yayin da lauyoyinsa ke neman sauyin wasu sharuddan belin.

Ya kuma ƙara da cewa iyalansa da lauyoyinsa ba su ga wata takardar kotu da ta ba da izinin tsare shi fiye da awanni 48 ba tare da gurfanar da shi ba, tare da zargin cewa sun fuskanci ƙalubale wajen samun damar ganawa da shi.

Haka kuma, Adekeye ya ce a ranar 17 ga Fabrairu, an hana ɗaya daga cikin matansa kai masa abinci kai tsaye, inda aka buƙace ta ta mika ta hannun wani jami’in hukumar. Ya ƙara da cewa washegari, 18 ga Fabrairu, an sauya masa wurin tsarewa daga EFCC zuwa ICPC ba tare da sanar da iyalansa tun da farko ba.

Da yake mayar da martani, Atiku ya ce idan har hukumomi ba za su iya tabbatar da lafiyarsa da kare masa haƙƙoƙinsa ba, to abin da ya dace shi ne a bada shi beli ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya kuma yi gargadin cewa yaƙi da cin hanci da rashawa bai kamata ya zama makamin siyasa ba. “Adalci dole ne ya kasance a bayyane, kuma doka ta yi aiki kan kowa ba tare da tsoro ko son rai ba,” in ji shi.

Comments (0)
Add Comment