Atiku Ya Tattauna da Shugaban Jam’iyyar ADP

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya gana da Shugaban Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), Yabagi Yusuf Sani, tare da wasu manyan jami’an jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa taron ya gudana ne ranar Asabar a gidan Atiku da ke Abuja.

Ganin jita-jitar da ke yawo kan yiwuwar haɗin kai tsakanin wasu ‘yan adawa kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, wannan ganawar na daga cikin abubuwan da ake lura da su sosai.

Ana ta rade-radin cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, na iya samun tikitin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu.

Wannan lamari na iya zama kalubale ga Atiku, wanda shi ma ke neman tikitin shugabancin kasa na ADC.

Sai dai, Shugaban jam’iyyar na ADP, Yabagi Yusuf, ya bayyana cewa ganawar da Atiku ya yi da su ba ta shafi haɗa jam’iyyu ba, har ma ya ƙara da cewa ba a yi taron ne don jawo wani mutum cikin ADP ba.

Comments (0)
Add Comment