Atiku ya zargi APC da yin aringizon kuri’u a zaɓen fidda gwani

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce babu kamshin gaskiya a adadin kuri’un da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a makon da ya gabata.

Atiku ya bayyana cewa ikirarin kuri’u miliyan da jam’iyyar ta ce Tinubu ya samu ba zai yiwu ba, yana mai cewa babu shakka “rubuta kuri’un aka yi” domin nuna wata irin gagarumar nasara da ba ta dace da hakikanin abin da ya faru ba.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar PDP ya ce irin wannan tsari na iya rage amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya da kuma sahihancin zaɓe a Najeriya.

Ya kuma yi zargin cewa jam’iyyun siyasa na amfani da alkaluman kuri’u wajen yaudarar jama’a da ƙoƙarin nuna ƙarfin da ba su da shi a zahiri.

Atiku ya buƙaci a riƙa gudanar da zaɓuɓɓuka cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa Najeriya na buƙatar shugabanci mai gaskiya da mutunta ra’ayin jama’a.

Sai dai kawo yanzu jam’iyyar APC ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye domin mayar da martani kan kalaman na Atiku ba.

Comments (0)
Add Comment