ATM Gwarzo Ya Janyewa Barau Takarar Kujerar Sanatan Kano Ta Arewa

Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, ya janye aniyarsa ta neman takarar Sanatan Kano ta Arewa bayan wani zaman sulhu da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranta a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce matakin ya biyo bayan tattaunawa tsakanin bangarorin siyasa domin samar da haɗin kai da fahimtar juna gabanin zaɓukan 2027.

Da wannan mataki, Barau Jibrin zai ci gaba da kasancewa ɗan takarar da ake marawa baya a kujerar Sanatan Kano ta Arewa.

Comments (0)
Add Comment