Majalisar zartarwa ta Australia ta amince da shirin da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi na sauƙaƙa wa jama’a da tallafin mai – wanda za ta kashe dala biliyan biyu da rabi.
Firaminista Anthony Albanese ya ce gwamnati za ta rage rabin kuɗin fito a kan man fetur da man gas na dizil tsawon wata uku.
Haka kuma ya buƙaci jama’a, da su riƙa amfani da ababan hawa na jama’a domin alkinta man don masana’antu da ke buƙatarsa.
A wasu wuraren kusan farashin man dizil ya ninka biyu tun bayan da aka fara yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
Daga ranar Lahadi wasu jihohi biyu a ƙasar ta Australia sun ɓullo da shirin wucin-gadi na sauƙaƙa wa jama’a hawa motoci da sauran ababan hawa na jama’a kyauta.