Shugaba Donald Trump ya ce bai ji daɗin yadda Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a Lebanon ba, bayan an amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.
Trump ya shaida wa manema labarai a wajen taron G7 cewa ya kamata Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya riƙa yin abu na masu hankali.
Ya ce an kashe mutane da dama a Lebanon, kuma babu buƙatar Isra’ila ta riƙa kai hare-hare kan gidajen farar hula don kawai suna neman wani ɗan Hezbollah.
“Ban ji daɗin abin da Isra’ila ta yi kan batun Lebanon da Hezbollah ba, ya kamata ace an yi an ƙare a ƙankanin lokaci, amma sai ga shi batun yana ɗaukar lokaci mai tsawo,” in ji shi.
Trump ya ce ya bayyana wa Isra’ila rashin jin daɗinsa a karon farko ne, bayan ta kai hari a Lebanon sa’a biyu gabanin Iran da Amurka su sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi.