Babban Editan Arewa Updates Ya Kare ‘Yancin Aikin Jarida

Babban Editan Arewa Updates, Bashir Sharfadi, ya mayar da martani ga masu sukar kafafen yaɗa labarai kan tambayoyin da suke yi wa gwamnati, yana mai jaddada cewa aikin jarida ba aikin kare gwamnati ba ne.

Sharfadi ya bayyana hakan ne bayan wata muhawara da ta biyo bayan tambayar da Sawaba FM ta yi kan inda aka kwana da kuɗaɗen fadama a Jihar Jigawa. Ya ce yin tambaya game da kuɗaɗen jama’a haƙƙi ne na ‘yan ƙasa da kuma kafafen yaɗa labarai.

Ya ce Sawaba FM ba ta zargi kowa da sata ko almundahana ba, sai dai ta nemi karin haske kan yadda aka gudanar da kuɗaɗen. A cewarsa, maimakon a ba da amsa kai tsaye, wasu jami’an gwamnati sun karkata hankali wajen sukar gidan rediyon da ma’aikatansa.

Sharfadi ya jaddada cewa aikin jarida shi ne bincike, tambaya da bayyana gaskiya ga jama’a, ba wai kare muradun gwamnati ko wata jam’iyya ba. Ya kuma yi gargadin cewa ɗaukar cewa kafafen yaɗa labarai dole ne su kare shugabanni saboda asalin yankinsu ko dangantaka da su na iya zama barazana ga dimokuraɗiyya.

Ya ƙara da cewa gwamnati mai gaskiya ba ta tsoron tambayoyi, domin abin da ya kamata ta yi shi ne gabatar da hujjoji da bayanai domin gamsar da jama’a.

A ƙarshe, ya yi kira da a bar ‘yan jarida su gudanar da aikinsu cikin ‘yanci da ƙwarewa, tare da kauce wa matsin lamba daga masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da gwamnati.

Comments (0)
Add Comment