Barcelona Ta Dauki Dan Wasan Masar Hamza Abdelkarim

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sanar da ɗaukar matashin ɗan wasan gaba na ƙasar Masar, Hamza Abdelkarim.

Barcelona ta tabbatar da cewa yanzu Hamza Abdelkarim ya zama cikakken ɗan wasanta bayan amfani da damar sayensa da ke cikin ƙunshin yarjejeniyar aronsa da ta ɗauka.

Abdelkarim, mai shekara 18, ya koma Barcelona ne a watan Janairun bana daga ƙungiyar Al Ahly a matsayin aro, inda ya buga wa ƙungiyar matasa ta Juvenil A wasanni a ƙarshen kakar wasa.

Matashin ɗan wasan ya zura ƙwallaye shida a wasanni 11 da ya buga, abin da ya sa Barcelona ta yanke shawarar ɗaukarsa na dindindin tare da ƙulla yarjejeniyar da za ta riƙe shi har zuwa shekarar 2029.

Ko da yake Barcelona ba ta bayyana kuɗin da aka sayi ɗan wasan ba, amma rahotannin kafafen yaɗa labarai na Spaniya sun ce an kammala cinikin ne kan kusan Yuro miliyan 1.5, baya ga wasu ƙarin tsarabe-tsaraben kuɗaɗen da suka danganci bajintar ɗan wasan.

A halin yanzu Abdelkarim na tare da tawagar ƙasar Masar a gasar Kofin Duniya, inda ya samu damar taka leda a wasannin da ƙasarsa ta buga da Belgium da kuma New Zealand.

Ana kallon Abdelkarim a matsayin ɗaya daga cikin matasan ’yan wasan da ake sa ran za su haskaka a nan gaba, bayan irin bajintar da ya nuna tun bayan komawarsa Barcelona.

Comments (0)
Add Comment