Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta shirya sauraron tayin masu bukatar yan wasan ta har kusan 12 da zarar an bude kakar wasanni ta bana.
Tuni har masu sharhin wasanni suka fara alaƙanta cefanar da yan wasan ne saboda kokarin kawo dan wasan gaba na Inter Milan Lautaro Martinez.
Daga cikin yan wasan da za a kadawa kararrawar dai akwai; Dembele da Coutinho, Samuel Umtiti, Junior Firpo, Ivan Rakitic, Neto, Nelson Semedo, Arturo Vidal, Martin Braithwaite, Carles Alena, Rafinha Alcantara da kuma Jean-Clair Todibo.
- Ana ci gaba da kaɗa ƙuri’a a zaben shugaban kasar Chadi
- An kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da jiragen yaki suka kai a Borno da Nijar
- Ministan Shari’a ya yi alkawarin sake duba dokar da ta haramta yunkurin kunar bakin wake a Najeriya
- Cibiyar ICAN ta karrama Gwamna Mallam Umar Namadi na Jihar Jigawa da lambar yabo
- Abba Kabir Yusuf ya musanta korar masu aikin tsaftace titi a jihar Kano
Shugaban ƙungiyar Jose Bartomeu ya zanta da mahukunta a kungiyar Inter Milan din kan ɗaukar ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Argentina.
Barcelona dai na cikin ƙaƙanakayi ta fuskar samun kuɗin shiga sanadiyyar annobar Korona, don haka kuɗin da zasu kashe ba shi da yawa kan yan wasa.
Jaridar Marca ta rawaito cewa Barcelona zata sanya kusan rabin yan wasanta a kasuwa don samun kuɗaɗen shiga da kuma samun zarafin kawo sabbin fuska kungiyar.
Amma sai dai sanarwar ta bayyana cewa ba duk yan wasan 12 ne zasu tafi a matsayin tafiyar din-din ba, wasu daga cikinsu zasu tafi ne a matsayin aro.