Hedkwatar Tsaron Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon gagarumin aikin soji mai suna Operation Clean Sweep III a ƙaramar hukumar Matazu da ke jihar Katsina, domin yaƙi da ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin.
A cewar rundunar, an fara aikin ne a ranar 14 ga Yuni, 2026, bayan kisan tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu a hannun ƴan bindigar da suka yi garkuwa da shi tare da matarsa.
Hedkwatar tsaron ta bayyana cewa manufar aikin ita ce kamo waɗanda ake zargi da hannu a kisan marigayin, da tarwatsa hanyoyin ayyukan ƴan ta’adda, tare da dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
Rundunar ta ce tun bayan ƙaddamar da aikin, dakarunta sun fara gudanar da sintiri da samame bisa bayanan sirri, tare da kai hare-hare a wuraren da ake zargin ƴan ta’adda ke buya.
Ta ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da tattara bayanai da gudanar da bincike domin tabbatar da cewa an kamo waɗanda ke da hannu a ayyukan ta’addanci da suka addabi yankunan.
A halin da ake ciki, an yi jana’izar marigayi Janar Rabe Abubakar a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, inda aka binne shi a makabartar Gidan Dawa da ke cikin birnin Katsina.
Hedkwatar tsaron ta jaddada aniyarta ta ci gaba da matsa lamba kan ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane, tana mai tabbatar da cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an cimma manufar aikin da kuma dawo da cikakken tsaro a yankin.