Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba

Yayin da ake cika shekaru 12 da sace ɗaliban makarantar Chibok su 272 da ƙungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014, ƙungiyar fafutukar BringBackOurGirls ta sake buƙatar gwamnati da hukumomi su bayyana inda ragowar ɗaliban da har yanzu ba a gano su ba suke.

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin ɗaliban da aka sace, 187 ne aka samu cetowa ko kuma suka tsere daga hannun masu garkuwa da su, yayin da har yanzu ba a san makomar ɗalibai 83 ba.

Ƙungiyar ta ce har yanzu iyalai da al’umma na ci gaba da rayuwa cikin damuwa da rashin tabbas kan makomar ‘yan matan, duk da shekarun da suka shafe ana gudanar da bincike da ƙoƙarin ceto su.

A cikin sanarwar da ta fitar, BringBackOurGirls ta jaddada buƙatar samun cikakken bayani kan halin da ragowar ‘yan matan suke ciki, tare da roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen gano gaskiya da kuma cika alkawuran da aka ɗauka tun farko.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa wannan batu ba wai na iya iyalan kaɗai ba ne, illa yana shafar ƙimar ɗan Adam da kuma martabar ƙasa baki ɗaya, tana mai cewa dole ne a kawo ƙarshen wannan rashin tabbas da ya daɗe ana fama.

Comments (0)
Add Comment