Mayakan Boko Haram sun kai farmaki a garin Magumeri na Jihar Borno a daren 22 ga Nuwamba, 2025, kimanin kilomita 45 daga Maiduguri.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun banka wa gidaje wuta, tare da lalata motocin jami’an Civilian Joint Task Force (CJTF). Wannan ya haifar da artabu mai zafi tsakaninsu da sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai, waɗanda daga bisani suka fatattaki maharan.
A halin yanzu, ba a tabbatar da yawan waɗanda suka rasa rayuka ba, sai dai mazauna yankin sun tabbatar da asarar rayuka da dukiyoyi na daruruwan miliyoyin naira.
Zulum Ya Ayana Rana Ta Musamman Don Azumi da Addu’a
Gwamnan Jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum, ya ayyana 24 ga Nuwamba, 2025, a matsayin rana ta musamman ta azumi da addu’a domin neman zaman lafiya da kawo ƙarshen hare-haren da suka ki ci suka ki cinyewa a jihar.
Tashin Hankali Ya Ƙaru a Watannin Ember
Rahotanni sun bayyana cewa watannin Ember (Satumba–Disamba) na bana sun yi muni, inda mutum sama da 700 suka rasa rayukansu a fadin ƙasar sakamakon hare-haren ta’addanci, ‘yan bindiga da rikice-rikice.
A ranar da aka kai harin Magumeri ma, an kashe mutane 10 a wani kwantan ɓauna da ake zargin Boko Haram suka kai kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.
Jami’an Tsaro Na Ci Gaba da Samame
Duk da cewa dakarun tsaro na ci gaba da kai hare-hare a mabuyar ‘yan ta’adda tare da kwato makamai, har yanzu ƙalubalen tsaro na ci gaba da tasowa lokaci zuwa lokaci.