Rahotanni daga Jihar Borno sun tabbatar da cewa mayaƙan Boko Haram sun kashe mutum biyar daga cikin mutane 416 da suka sace daga al’ummar Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
Wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta ya nuna gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe, inda aka ce sun rasa rayukansu ne bayan yunƙurin tserewa daga hannun masu garkuwar.
Ƙungiyar matasan Borno ta Kudu (BOSYA) ta bayyana cewa har yanzu mata da yara da dama suna a hannun ƴan ta’addan cikin mawuyacin hali.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati, ƴan siyasa da ƙungiyoyin jin ƙai da su haɗa kai domin ganin an ceto mutanen da aka sace kafin lamarin ya ƙara muni.