Boko Haram Sun Sace ’Yan Mata 14 a Askira Uba Yayin Aikin Gona

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun yi garkuwa da ’yan mata 14 a yankin Mussa, da ke Karamar Hukumar Askira Uba ta Jihar Borno, a lokacin da suke aikin gona.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar, inda ya ce maharan sun kai farmaki kan gonakin mutanen yankin a lokacin da matan ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

A cewar sanarwar, tuni jami’an tsaro – ’yan sandan Najeriya, sojojin Operation Hadin Kai, CJTF, da mafarauta – suka shiga dajin domin bin sahun maharan.

Rundunar ta tabbatar da cewa an ceto daya daga cikin matan, yayin da ake ci gaba da bincike da farautar maharan domin gano sauran 13 da ke hannunsu.

Sanarwar ta tabbatar cewa jami’an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dawo da sauran matan lafiya.

Comments (0)
Add Comment