Wani jigo a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya ce abin da mutane da dama ba su sani ba shi ne marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya taimaka wajen tabbatar da cewa Abba Yusuf ya zama gwamnan Jihar Kano.
Ya bayyana cewa Allah ne ya yi amfani da Buhari wajen tabbatar da cewa nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu a zaben 2023 ba a sace ta ba kamar yadda aka ce an yi a zaben 2019 ta hannun jam’iyyar APC.
Da yake magana a tashar Arise News, Galadima, wanda shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu (BoT) na NNPP, ya ce Buhari ba zai iya goyon bayan yunkurin Ganduje na kwace nasarar NNPP da ta Abba Yusuf ba, domin Ganduje ya taba cin mutuncin Buhari a baya.
Ya ce:
“Abin da yawancin ’yan Najeriya ba su sani ba shi ne Janar Buhari ne ya kwace nasararmu a 2019 ya ba Ganduje. Janar Buhari ne ya zama ginshikin da ya sa Abba Kabir Yusuf ya zama gwamnan Jihar Kano.
“Duniya ta kamata ta sani, domin Abba Yusuf ya bar gidan Allah ya tafi gidan Tinubu. Ya bar Allah ya rungumi dan Adam,” in ji tsohon abokin Buhari.
Ya kara da cewa:
“Ganduje ne da bakinsa ya zagi Buhari, duk da cewa Buhari ne ya kwace nasararmu ya ba shi a 2019. Ya kira shi ‘Abuna Abu’. Abuna Abu waka ce da shahararren mawakin Hausa Alhaji Hadi Mohammed na Katsina ya rera, wadda ke nufin mashayi mai lalata da mutunci, wanda zai sha giya ya rika yawo tsirara a titi ko ya kwanta a kasa ko karkashin itace.
“Wannan ne sunan da Ganduje ya kira Janar Muhammadu Buhari ba tare da ambaton sunansa kai tsaye ba. Buhari ya ji haushi matuka. Lokacin da muka ci zabe kuma suka so kwace shi, Magaji Bichi tsohon Daraktan DSS idan yana tsoron Allah, zai iya bada labarin gaskiya. Kuma idan ya rubuta tarihinsa (memoir), ya kamata ya saka wannan a ciki.
“Buhari ya tsaya daram ya ce: ‘Wannan yaron ya ci zabe a 2019 mun kwace masa. Yanzu ya sake cin zabe, ku ba shi nasararsa.’ Kun ga yadda Allah ke aiki? Ni Buba Galadima, yau na fara fadar abu mai kyau game da Buhari.
“An kai mu kotu, Kotun sauraron kararrakin zabe (Tribunal) ta yanke hukunci a mana. Ina gaya wa duniya yau, an sace alkalai aka kai su Abuja aka ba su hukunci rubuce. Aka ce mun sha kaye. Mun je Kotun Daukaka Kara (Court of Appeal), aka tsoratar da ita muka sha kaye. Mun je Kotun Koli (Supreme Court). Alkalai uku daga cikin biyar suka ce ba za su jawo zubar da jini a Kano ba.
“Suka ce Abba Yusuf ya ci zabe a 2019 amma an kwace masa da karfi, kuma bangaren shari’a bai taimake shi ba. Wannan karon ba za su zama hujjar zalunci ba, don haka aka tabbatar da Abba Yusuf a matsayin gwamna ta hanyar kotu da kuma taimakon Buhari.
“Wannan yana nuna cewa Allah ne ke aiki. Yanzu suna gaya wa mutane cewa ko da mun ci zabe a 2027, APC za ta kwace shi. To me ya sa ba za mu shiga jam’iyyarsu ba? Ma’ana shi (Abba Yusuf) ya bar dogaro da Allah wajen yin adalci, ya koma dogaro da APC da Shugaba Tinubu domin su ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara. Amma wannan nasara ta dan lokaci ce. Allah zai hukunta shi.”