Tsohon Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (rtd), ya shawarci gwamnatin tarayya da ta rufe iyakokin ƙasar kamar yadda aka yi lokacin annobar COVID-19, domin yakar ta’addanci da matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara.
Buratai ya bayyana hakan ne a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce barin ta’addanci ya ci gaba na da hadari ga makomar ƙasa, kuma ya zama wajibi a zuba jari wajen magance matsalar.
Ya jaddada cewa sojoji ba matsala ba ne, illa mafita ga rikicin tsaro, yana mai cewa an dade ana gargadi kan cewa rikicin zai ɗauki lokaci idan ba a ɗauki mataki ba.