Canjin Mulki Kaɗai Ne Zai Ceci Iran – Shugaban Kasar Isra’ila

Shugaban ƙasar Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana cewa Iran ba ta da wata makoma mai ɗorewa sai an samu sauyin shugabanci.

Herzog ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a Iran, inda jama’a ke nuna adawa da shugabannin addini na ƙasar.

Da yake magana a ranar Alhamis yayin wata hira a taron tattalin arzikin duniya (World Economic Forum) da aka gudanar a Davos, ƙasar Switzerland, Herzog ya ce wannan tarzoma mai yaɗuwa alama ce ta gagarumar damuwa da takaicin da jama’a ke ciki.

“Abin da ya fara a matsayin zanga-zanga kan matsin tattalin arziki ya rikide zuwa babban ƙalubale ga tsarin addini da ke mulkin Iran tun shekarar 1979.

“Mutanen Iran na marmarin canji. Mutanen Iran sun cancanci canji,” in ji Herzog.

Ya jaddada cewa gyara na gaske kuma mai ɗorewa ba zai yiwu ba sai an samu sauyin shugabancin siyasar Iran, yana mai nuna cewa dole ne irin wannan sauyi ya fito daga cikin Iran kanta, tare da goyon bayan ƙasashen duniya, ba tare da tilastawa daga waje ba.

“Makomar mutanen Iran tana cikin sauyin mulki kaɗai, kuma dole ne hakan ya kasance a hannun mutanen Iran tare da goyon bayan al’ummar duniya,” in ji shi, yana ƙara da cewa shugabancin addini na Iran na nuna alamun rashin kwanciyar hankali.

An fara manyan zanga-zanga a sassan Iran daban-daban tun daga ranar 8 ga Janairu, inda dubban mutane suka fito kan tituna tsawon kwanaki da dama a jere.

Tun daga bisani dai zanga-zangar ta ragu, abin da masu fafutuka suka danganta da tsauraran matakan da gwamnati ta ɗauka, ciki har da kama mutane da yawa da kuma katse intanet gaba ɗaya.

Comments (0)
Add Comment