, inda ta kashe aƙalla mutane bakwai tare da kwantar da kusan mutane 200 a asibiti.
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya ce cutar ta fara tun a ranar 10 ga watan Agusta, kuma tana ƙara yaɗuwa.
Ya bayyana cewa rashin tsaftar muhalli da ruwan sama sun taimaka wajen yaɗuwar cutar, musamman a inda ‘yan gudun hijira suke zaune.
Ya yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, cutar na iya zama annoba.