Cutar Limoniya tana kashe kananan yara a sassan Jihar Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ya yiwa Kungiyoyin Cigaban Fannin Lafiya Shagube kan yadda suka yi watsi cutar Limoniya wanda take kashe Kananan Yara a sassan Jihar nan.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Jiha Dr Salisu Mu’azu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar gudunmawar kayan gwaje-gwajen na Kanana da Manyan Asibitoci wanda Kungiyar Save the Children International ta bayar.

A cewarsa, Mafiya yawan Kungiyoyin Agaji na Kasashen Duniya da suke kawowa Jihar nan tallafi sun manta da cutar Limoniya, inda sukafi mayar da hankali kan Cutar Maleria, da HIV da Cutar Tarin Fuka da kuma rashin abinci mai gina jiki.

Dr Salisu Mu’azu, ya bukaci Kungiyoyin tallafin su yi aiki tare da gwamnati dom yakar cutar Limoniya domin bunkasa fannin Lafiyar Jama’a na Jihar Jigawa.

Da yake bayar da Jawabi, Shugaban Shirin Dr Adamu Isah, ya ce manufar bayar da tallafin shine domin cike gibin da yake tsakanin fannin Lafiya da kuma hanyoyin magance matsalolin da suke addabar fannin a Cibiyoyi 33 na Karamar Hukumar Kiyawa.

Comments (0)
Add Comment