Cutar Zazzabin Lassa (Lassa Fever) Ta Kashe Mutum Daya A Jihar Jigawa

An tabbatar da bullar cutar Zazzabin Lassa wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum guda a Jihar Jigawa, yayin da aka sanya wasu mutane da dama ƙarƙashin kulawar jami’an lafiya domin dakile yaduwar cutar.

Tawagar gaggawa ta Jihar Jigawa (Rapid Response Team) daga Sashen Lafiyar Jama’a na Ma’aikatar Lafiya, ƙarƙashin jagorancin Dr. Sabiu Aliyu na WHO/APHO, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba bayan gudanar da bincike a Asibitin Babura General Hospital.

Dr. Aliyu ya ce,

“Marigayin mazaunin ƙauyen Gari Uku ne da ke Ƙaramar Hukumar Babura, kuma an kwantar da shi a Babura General Hospital tare da alamomin cutar Zazzabin Lassa.”

Daga bisani aka tura majinyacin, mai suna Habibu Haruna, zuwa Asibitin Koyarwa na Danmasara (Danmasara Teaching Hospital), inda gwaje-gwajen dakin bincike suka tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar.

Bincike ya nuna cewa Haruna ya yi tafiya kwanan nan zuwa Saminaka a Ƙaramar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

Dr. Aliyu ya bayyana matakan da aka ɗauka na shawo kan lamarin, inda ya ce:

“An tanadar da muhimman magunguna da kayan kariya na likitoci (PPE) zuwa Babura General Hospital, sannan an fara bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da majinyacin tare da sanya su ƙarƙashin kulawa.”

Ya ƙara da cewa:

“Al’ummar da marigayin ya fito daga cikinta, da kuma ma’aikatan lafiya da suka kula da shi, suna ƙarƙashin kulawa a tsawon lokacin da cutar ke iya bayyana (incubation period).”

Comments (0)
Add Comment