Da Dumi-Dumi: Matatar Dangote Ta Kara Sauke Farashin Fetur

Matatar Dangote ta sake rage farashin fetur da take sayarwa ga dillalai (gantry price) daga Naira 1,175 zuwa Naira 1,125 kan kowace lita a faɗin ƙasar nan.

Mai magana da yawun Kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya tabbatar da sabon ragin farashin a ranar Alhamis, yana mai cewa an rage farashin da Naira 50 kan kowace lita.

“Hakika mun rage farashin fetur da Naira 50 kan kowace lita,” in ji Chiejina.

Haka kuma, farashin fetur da matatar ke fitarwa ta ruwa ya sauka daga Naira miliyan 1.495 zuwa Naira miliyan 1.428 kan kowace metric tonne.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya sauka zuwa tsakanin dala 69 da dala 73 kan kowace ganga, matakin da ya yi daidai da wanda ake samu kafin rikicin Gabas ta Tsakiya.

A ranar 16 ga Yuni, 2026, matatar Dangote ta rage farashin fetur da Naira 75 kan kowace lita, lamarin da ya haifar da saukar farashin mai a gidajen mai a sassa daban-daban na ƙasar.

Da wannan sabon ragi, jimillar rage farashin da matatar ta yi cikin makonni biyu ya kai Naira 125 kan kowace lita.

A halin yanzu, ana sayar da fetur tsakanin Naira 1,241 da Naira 1,305 kan kowace lita a Abuja da kewaye.

Sai dai da dama daga cikin ‘yan Najeriya na ci gaba da kira da a ƙara rage farashin fetur zuwa tsakanin Naira 800 da Naira 900 kan kowace lita, kamar yadda yake kafin tashin rikicin Iran da Isra’ila da Amurka a farkon shekarar 2026.

Comments (0)
Add Comment