Dalilan da yasa kotu ta ki amincewa da bukatar belin Abba Kyari

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau ta ki amincewa da bukatar belin mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a wani hukunci da ya yanke, ya ce bukatar ta biyo bayan umarnin wata kotu da ta bayar, inda ta baiwa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA damar cigaba da tsare Abba Kyari na tsawon kwanaki 14 domin ta kammala bincike.

Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa kotun wacce ta bayar da wannan dama ga hukumar NDLEA a ranar 22 ga watan Fabrairu, kotun ce mai zaman kanta.

Alkalin kotun, ya ce ya na son sauraron karar da Abba Kyari ya shigar na tabbatar da hakkinsa bayan karewar wa’adin kwanaki 14 na kotu.

Daga nan sai ya dage zaman kotun har zuwa ranar 15 ga Maris don sauraron bukatar Abba Kyari na neman a tabbatar masa da hakkinsa.

Comments (0)
Add Comment