Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a jam’iyyar PDP, Umar Danjani Hadejia, ya miƙa ƙorafi (petition) ga Kwamitin Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Majalisar Wakilai, inda ya buƙaci a gudanar da bincike kan amincewar da aka bayar na kashe Naira 470,312,500 domin kwaso taraktoci 100 da kayayyakin noma daga Abuja zuwa Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
A cikin wasiƙar ƙorafin mai ɗauke da kwanan wata 24 ga Yuni, 2026, Umar Danjani ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne a matsayinsa na ɗan ƙasa mai kishin jihar, domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma kare dukiyar al’umma.
Ya ce adadin kuɗin da aka amince da shi ya tayar da tambayoyi a tsakanin jama’a, musamman dangane da ko kuɗin ya yi daidai da farashin kasuwa da kuma ko an bi ƙa’idojin da suka dace wajen ƙididdigewa da bayar da kwangilar jigilar kayan. A saboda haka ne ya nemi Majalisar Wakilai ta binciki tushen amincewa da kuɗin da kuma yadda aka ƙayyade su.
Danjani ya kuma roƙi kwamitin da ya tabbatar da sahihancin tsarin saye da ƙididdigar kuɗaɗen da aka yi amfani da su, tare da tantance ko adadin da aka ware ya dace da ainihin kuɗin da ake kashewa a irin wannan aiki.
Ya jaddada cewa ƙorafin da ya gabatar ba domin cin mutuncin gwamnatin Jigawa ko tayar da ƙura ba ne, sai dai domin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan shugabanci a harkokin tafiyar da kuɗaɗen jama’a.
Lamarin dai na zuwa ne yayin da Gwamnatin Jihar Jigawa ke ci gaba da aiwatar da manyan shirye-shiryen bunƙasa harkar noma, ciki har da samar da taraktoci da sauran kayan aikin gona ga manoma a faɗin jihar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Gwamnatin Jihar Jigawa dangane da ƙorafin da Umar Danjani ya gabatar wa Majalisar Wakilai.