Dole Sai Mun Lalata Uranium Din Iran Za A Dakatar da Yaƙi – Netanyahu

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu, ya ce dole ne a lalata sinadarin Uranium da Iran ta ke da shi, sannan za a kawo ƙarshen yaƙinta da Amurka da Isra’ila.

Wannan na daga cikin abin da Firaministan ya faɗa a wata hira da za a saki da shi anjima.

“Wannan [yaƙin] bai ƙare ba tukuna, saboda makaman nukiliya, tataccen uranium ɗin, dole ne a fitar da su daga Iran. Wuraren da ake amfani da su dole ne a wargaza su,” kamar yadda ya faɗa a cikin wata hira da gidan talabijin na CBS.

Ya ƙara da cewa: “Har yanzu Iran tana goyon bayan dakarun juyin juya hali da ƙera makamai masu linzami. Yawancin waɗannan an lalata su, amma akwai sauran aiki.”

Da aka tambaye shi ta yaya za a fitar da wannan Uranium ɗin, Mista Netanyahu ya ce: “Ku kuka shigo da kuma ku za ku fitar da shi.”

Comments (0)
Add Comment