EFCC: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Kadarorin Da Ake Dangantawa Da Malami Ranar 6 Ga Yuli

Kotu za ta yanke hukunci ranar 6 ga watan Yuli kan shari’ar ƙwace kadarori 57 da ake dangantawa da tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, bayan da hukumar EFCC ta zarge su da kasancewa kuɗaɗen haramtattun ayyuka.

Lauyan EFCC, Jibrin Okutepa SAN, ya roƙi kotu ta tabbatar da ƙwace kadarorin ga Gwamnatin Tarayya, yana mai cewa waɗanda ake ƙara sun kasa tabbatar da cewa kadarorin an same su ta halal.

Sai dai lauyan Malami, Adedayo Adedeji SAN, ya musanta zargin, yana cewa EFCC ta dogara ne da zato ba tare da hujjoji ƙwarara ba, tare da jaddada cewa wasu daga cikin kadarorin an mallake su tun kafin Malami ya shiga gwamnati.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga Yuli domin yanke hukunci.

Comments (0)
Add Comment